SARAUTAR XANRIMI A MASARAUTAR KANO

Garba Saleh Kwalejin Ilimi Ta Amana, Qunchi (ACOE QUNCHI KANO)
Volume 5(1), January 2014

Abstract

Wannan takarda mai taken Sarautar Xanrimi a Masarautar Kano, an shirya ta ne da nufin bincikowa tare da bayyana asalin samuwar wannan sarauta mai matuqar muhimmanci a kan sha'anin Fada. Hanyoyin nema da kuma tattara bayanan binciken sun haxa da karancekarancen rubuce-rubucen da suke da nasaba da fada, musamman ta Kano, da tattaunawa da mutanen da suka san fada da kuma ziyartar fada domin lura da sha’anoninta musamman waxanda suka shafi sarautar Xanrimi. Sakamakon binciken ya zo da salsalar sarautar Xanrimi da waxanda suka riqe ko suke riqe da sarautar da ayyukan basaraken da makusantansa, kamar hakimai, da kuma matsayin sarautar a Masarautar Kano