GINSHIQAN KOYAR DA HAUSA DON CI GABAN qASA

Umar Yahaya Sashen Koyar da Hausa Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi Kumbotso, Jihar Kano, Nijeria
Volume 5(1), January 2014

Abstract

Manufar wannan takarda ita ce bincikowa tare da yin tsokaci a kan ingantattun ginshiqan koyar da Hausa don ci gaban qasa. Daga cikin ginshiqan koyar da Hausa da takardar ta gano, ta keve ingantaccen malami a matsayin jagora, wato wanda ya fi sauran muhimmanci. Sannan ta binciko tare da bayyana abubuwan da suke sawa malami ya zama ingantaccen ginshiqin koyar da Hausa. Sakamakon binciken ya bayyana abubuwa kamar: qwarewar malami a fannonin nazarin Hausa; samun horo tare da sanin dabarun koyarwa; kasancewar malami abin koyi; samun horo tare da sanin fannin halayyar xan’adam; yawaita bincike da nazarce-nazarce; kiyaye dokoki da sharuxxan aiki; nunawa tare da tabbatar da adalci tsakanin xalibai. An tattara bayanan wannan bincike ne ta hanyoyi biyu, wato ta hanyar karance-karance da kuma lura da malamai yayin da suke koyarwa. Haka kuma an tattauna da wasu mutane tare da musayar ra’ayoyi dangane da muhimman batutuwa